22 Yuni 2020 - 09:46
Majalisar Dokokin Iran, Ta Yi Tir Da IAEA

Majalisar dokokin jamhuriyar musulinci ta Iran, ta yi allawadai da kakkausar murya da kudirin baya baya nan na majalisar gwamnonin hukumar yana yaduwar makamman nukiliya ta duniya (IAEA).

(ABNA24.com)  Majalisar dokokin jamhuriyar musulinci ta Iran, ta yi allawadai da kakkausar murya da kudirin baya baya nan na majalisar gwamnonin hukumar yana yaduwar makamman nukiliya ta duniya (IAEA).

A wata sanarwa da majlaisar ta fitar mai dauke da sa hannun mambobinta 240 sun yi tir da abunda suka danganta da nuna wariya a hukumar.

Iran, ta bada misali da wani rahoton hukumar ta IAEA, dake cewa, a cikin shekaru shiga da suka gabata, damar data baiwa hukumar na gudnar da bincike ya karu daga kashi 4% zuwa 20% a Iran.

A wani share kuma Iran, ta gode wa kasashen da suka ki goyan bayan kudirin data danganta da abun kunya, da kuma matsin lamba daga abokan gabanta wanda a cewarta ba zai haifar da da mai ido ba.


/129